">
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
Sunday, October 12, 2025
No Result
View All Result
NEWSLETTER
Daily Episode Hausa
-18 °c
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu
No Result
View All Result
Daily Episode Hausa
No Result
View All Result
">

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane Sama Da 40 A Jihar Filato

by Maryam Umar Said
August 4, 2021
in Best Store, Technologies
0
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane Sama Da 40 A Jihar Filato
Share on FacebookShare on Twitter
">

RelatedPosts

Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 6 a Sakkwato

An kama matar da ake zargi da kai wa Bello Turji makamai daji a Zamfara

An Kashe Shahararren Dan Ta’adda Gwaska, Yayin Da Mazauna Yakin Yantumaki Ke Hijira Kan Tarar N30m Da Barazanar Kisa

Shugaba Buhari Ya Bukaci Shugabannin Tsaro Su Kawo Sabbin Dabaru Kan Tsaron Kasar Nan

">

A karo na biyu, mahara sun kai hari kan wasu al’umomi a masarautar Miango ta jihar Filato ranar Litinin wanda ya janyo rasa rayuka da asarar dukiya mai dumbin yawa.

Tun ranar Asabar ne wasu ‘yan bindiga suka fara afka wa kananan hukumomin Bassa da Riyom na jihar, inda suka kona daruruwan gidajensu, baya ga barnata amfanin gona a yankin.

Rahotanni daga kafofin yada labarai a Najeriya na cewa kimanin gawa 43 aka gano zuwa safiyar yau Talata a wasu kauyukan da ke masarautar Irigwe da ke karamar hukumar Miango.

Shugabannin masarautar Iregwe, wadanda hare-haren suka fi shafa sun koka kan yadda jami’an tsaro suka kyale maharan su ci gaba da kai hare-haren da suka shafe kwana uku suna ka wa a yankin.

Prince Robert Irigwe Ashidodo, shugaban kungiyar raya masarautar Iregwe ya shaida wa BBC Hausa cewa jami’an tsaron da aka tura yankin sun ki daukar mataki kan maharan duk da cewa mazauna kauyukan sun sanar da su halin da suke ciki.

Mista Dan Manjang wanda shi ne kwamishinan yaɗa labarai na jihar ta Filato, ya faɗa wa BBC Hausa cewa duk da cewa tsaron rayuka ya rataya a wuyansu amma harkar tsaro ta dukkan jama’ar gari ce.

Duk ƙoƙarin da BBC ta yi na ji daga bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Filato bai yi nasara ba saboda yana mai bayar da uzurin cewa yana asibiti wajen duba maras lafiya.

A ranar Litinin Auta Danjuma, wani jigo a masarautar Irigwe, ya shaida wa BBC cewa suna zargin Fulani makiyaya da kai hare-haren. Sai dai Muhammadu Nura Abdullahi, shugaban kungiyar Mi Yetti Allah ta Fulani makiyaya a jihar Filato, ya musanta zargin.

DAILY EPISODE HAUSA

KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER

">
Maryam Umar Said

Maryam Umar Said

Related Posts

hallaka ’yan ta’adda

Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 6 a Sakkwato

by Abubakar Ismail kankara
January 18, 2025
0

Sojojin rundunar Operation Hadarin Daji sun hallaka ’yan ta’adda shida a wani artabu da ya faru a karamar hukumar Gudu,...

An kama matar da ake zargi da kai wa Bello Turji makamai daji a Zamfara

An kama matar da ake zargi da kai wa Bello Turji makamai daji a Zamfara

by Abubakar Ismail kankara
December 30, 2024
0

Bataliyar rundunar sojin Najeriya mai yaƙi da yan fashin daji a arewa maso yammacin Najeriya da ake kira da Operation...

yan bindiga

An Kashe Shahararren Dan Ta’adda Gwaska, Yayin Da Mazauna Yakin Yantumaki Ke Hijira Kan Tarar N30m Da Barazanar Kisa

by Abubakar Ismail kankara
February 11, 2022
0

Sama da mutane dubu daya mazauna kauyen Tashar Biri suka tsere daga kauyen da ke Yatumaki a karamar hukumar Dan...

Buhari Ya Nemi Shugabannin Tsaro Su Kawo Sabbin Dabaru Kan Tsaro

Shugaba Buhari Ya Bukaci Shugabannin Tsaro Su Kawo Sabbin Dabaru Kan Tsaron Kasar Nan

by Maryam Umar Said
September 8, 2021
0

A zaman da ya wakana a jiya Talata a fadar shugaban kasa kan yanayin tsaron kasar nan, shugaba Buhari ya...

Hadin Kan Gwamnonin Arewa Da Sasanci Da Ýan Ta'adda Zai Kawo Zaman Lafiya - Masana

Sasanci Da Ýan Ta’adda Da Hadin Kan Gwamnoni Zai Kawo Zaman Lafiya – Masana

by Maryam Umar Said
September 8, 2021
0

Shugaba kuma mawallafin jaridar Blueprint, Muhammad Idris, ya bayyana cewa sasanci da ýan ta'adda da kuma samun daidaiton ra'ayi tsakanin...

Ýan Bindiga Sun Kai Sabon Harin Da Suka Yi Garkuwa Da Mutane 18 A Kaduna

Ýan Bindiga Sun Kai Sabon Harin Da Suka Yi Garkuwa Da Mutane 18 A Kaduna

by Maryam Umar Said
September 7, 2021
0

Ýan bindiga sun kai sabon hari a unguwar Keke da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna. Ýan bindigar sun...

Next Post
Manyan APC Da PDP Sun Mayarwa Farfesa Jega Martani

Manyan APC Da PDP Sun Mayarwa Farfesa Jega Martani

Allah Ya Yiwa Mahaifiyar Aminu Ala Rasuwa

Allah Ya Yiwa Mahaifiyar Aminu Ala Rasuwa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

">
  • Talla
  • Tuntube Mu
  • Gida
TUNTUBE MU: 08032398985 info@dailyepisode.ng

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Tsaro1
  • Bincike
  • Siyasa
  • Qalubalen Mu
  • Aiki/Sana’a
  • Ra’ayi
  • Tuntube Mu

Copyright © 2025 DAILY EPISODE HAUSA Designed by AIACCESS CONTRACTORS

Login to your account below

Forgotten Password?

Fill the forms bellow to register

All fields are required. Log In

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In