Mazauna unguwar Rigasa dake qaramar hukumar Igabi jihar Kaduna, sun gamu da annobar zaizayar qasa da kuma ambaliyar ruwa.
Inda hakan yayi sanadiyyar asarar gidaje da dama a daura road da bayan wuya, hakan ya tursasawa mazauna wurin barin gidajensu da zama ýan cirani a gurare daban daban.
Yanayin ya fara aukuwa ne lokaci mai tsawo, kamar yadda mazaunin unguwar sagir umar ya bayyana cewar a yankin bayan wuya, hadamammun masu lambukane suke toshe hanyoyin ruwan don qara girman lambunsu, ba tare da duba da hadarin hakan ga rayuka da kadarorin alumma ba.
Mazaunan daura road, sun shiga hadarin zabtarewa da zaizayewar qasa ne sanadiyyar cire wasu tsoffin manyan bishiyun mangwaro guda biyu da akayi a yankin, har ya kaiga samar da qaton kududdufin da ya taimakawa zabtarewar qasar da hadiye gidajen jama’a.
Bayan faruwar lamarin, rashin hanyar ruwa a yankin ya taimaka matuqa wajen ci gaba da zaizayewar qasar da yake cinye gidajen mazauna yankin.
Mazauna yankin sun rubuta takardu da dama zuwa ga qaramar hukuma, gwamnatin jiha, ecological fund da kuma ma’aikatar kula da muhalli ta qasa, game da halin da suke ciki akan a taimaka musu amma haqan su bai cimma ruwa ba.
A qarqashin shugabancin Dr. Muhammad Mahmood Abubakar ne, a shekarar 2019 ma’aikatar kula da muhalli ta qasa ta turo ma’aikata tare da alqawarin shiga lamarin.
A disambar 2020 ne, ma’aikata suka zo suka fara aiki sai dai kash! Ba aje ko ina ba suka kwashe kayansu suka qara gaba, inda hakan ya qara ruruwar zaizayar qasar da ambaliya.
Rashin qarasa aiki ba baqon abu bane ga gwamnati, wanda hakan yana cutar da al’ummarta matuqa.
Mazauna yankin suna cikin hadari babba saboda gurbatacciyar iska da ruwa da rashin hanya.
Wasu daga cikin mazauna Abuja road sunyi qoqarin nemawa kansu mafita, ta hanyar bude hanyar ruwan da fatan hakan zai kawo musu sauqin ambaliyar ruwan da ya addabi gidajensu.
