An harbe mutum biyu da ake zargin masu satar mutane ne, a lokacin da suka je karbar kudin fansa a garin Sabongida da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, wadanda ake zargin sun sace wani tsoho mai suna Alhaji Gambo.
Masu garkuwa da mutanen wato Sani da Musa, sun umarci iyalan Alhaji Gambo, su kai kudin fansa inda wani wuri, don haka aka shaidawa ‘yan kato da gora inda suka je dajin sukai musu kwantan bauna.
Jaridar ta ce masu satar mutanen dauke da muggan makamai, sun isa wajen, ba tare da sun san an yi musu kwantan bauna ba, inda ‘yan kato da gorar suka bude musu wuta a lokacin da suka sunkuya domin daukar kudin.
Nan take aka kubutar da tsohon, wanda daman sun zo karbar kudin fansar tare da shi.
Wani mazaunin garin ya shaidawa Daily Trust cewa, masu garkuwa da mutanen sun kashe mutane da dama a kauyen Borno-Korokoro, daTella, da Sabongida, da Dananacha, Jalingo zuwa Wukari da ke jihar Taraba.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, ASP Abdullahi Usman,ya tabbatar da faruwar lamarin da kisan masu garkuwa da mutanen sai dai bai kara cewa komai bayan hakan ba.