Najeriya ta karbi tallafin allurar riga-kafin cutar korona miliyan hudu daga gwamnatin Amurka.
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, ya ce tallafin riga-kafin wani bangare ne tallafin allurar guda akalla miliyan 25 cikin miliyan 80 da za a rabawa kasashen nahiyar Afurka.
Amurka ta miƙa alluran karkashin shirin Covax, inda aka mika ga jami’an gwamnatin Najeriya a babban birnin kasar Abuja.
Hukumomin Najeriya sun ce, ana fatan riga-kafin samufurin Moderna za su kara ƙaimi wajen ganin an yi wa ‘yan kasar riga-kafin cutar korona.
Kawo yanzu kashi 1 cikin 100 na al’ummar kasar miliyan 200, aka yi wa rigakafin korona samufurin , da ita ma aka karba karkashin shirin Covax a watan Maris.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun karuwar masu kamuwa da cutar Korona a kowacce rana , kuma na sabon nau’in Delta.
Jami’ai a Najeriyar na cewa an shiga zagaye na uku na barkewar cutar a kasar.
KU BIYO MU A FACEBOOK DA TWITTER