Ƙungiyar iyayen yaran da aka sace a Kano ta zargi kwamitin da gwamnati ta ɗora wa alhakin gano sauran yaran da aka sace a jihar daga shekarar 2010 zuwa 2019 da jan ƙafa wajen fitar da sakamakon gwajin ƙwayar hallitta da aka yi wa yaran don tantancewa.
Koken ƙungiyar na zuwa ne bayan da a makon da ya gabata wata kotu da ke jihar Kanon ta yankewa Mista Paul da ake zargi da sace yaran jihar yana safarar su zuwa jihohin kudancin Najeriya, hukuncin ɗaurin sama da shekara 100 a gidan kaso.
Sakataren kungiyar iyayen da aka sace wa ƴaƴa, Shu’aibu Ibrahim Tajiri, ya shaidawa BBC cewa tsawon lokacin da aka ɗiba wajen samar da sakamakon gwajin kwayar hallittar yara 10 da aka gano a jihar Anambra, ya nuna cewar kwamitin ba da gaske yake aikinsa ba.
Tajiri ya ce kimanin wata shida kenan da daukar ƙwayoyin hallatar yaran da aka gano a jihar ta Anambra, amma sun gaji da yau da gobe da yan kwamitin ke yi musu, inda suka ce da rabon kwamitin ya zauna an fi wata uku.
To sai dai a cewar kwamitin gano inda yaran da aka sacen suke, ya ce suna aiwatar da shawarwarin da suka bai wa gwamantin jihar kusan guda 40, ya ce suna aiki tuƙuru kan batun dawo da yaran kuma suna da gwajin kusan yara 6 daga cikin wadanda aka dauki kwayoyin hallartar tasu.
Sai dai kwamitin ya ce suna ci gaba da neman wata mata mai suna Amina Kagara wadda ta tsere tun bayan da aka bayar da ita belinta.
A makon da ya gabata ne dai wata babban kotun a Kano ta yanke wa Paul Owne, jagoran wadan da ake zargi da sace yara a Kano tare da sayar da su jihohin kudu hukuncin daurin shekaru 104 a gidan gyaran hali, bisa zargin aikata lafuka 38.
Haka zalika a ranar 31 ga watan Disambar bara ne dai iyayen wasu yara fiye da 100 da suka nemi ‘ƴa ‘ƴansu sama ko ƙasa a jihar Kano s ka gudanar da wata zanga-zanga tare da nuna damuwarsu kan yadda gwamnatin jihar ke jan kafa wajen ceto musu ‘ya’yan nasu.
Daga bisani a farkon shekarar da muke ciki ta 2021 gwamanti Kano ta bakin kwamishinan yada labaran jihar Mallam Muhammad Garba tace ta gano karin wasu yara 10 a jihar Anambra, kuma ta aike da jakadu dan tantance yaran na Kano ne.
Daga bisani, aka ce sai an yi gwajin kwayar hallitta, saboda samun wasu dake ikirarin wasu daga cikin yaran na Anambra ‘ya’yansu ne da suka bata.